HADISAN HULƊA DA SHUGABANNI DA NAUYINSU A ZUKATAN MUTANE A YAU
Hadisan Manzon Allah (SAW) ingantattu sun zo birjik don bayani akan yadda ya kamata musulmi ya yi hulɗa da shugabanni. Galibin hadisan sun ayyana cewa za a yi wasu shugabanni macuta, masu aiki da saɓanin shiriyar Manzon Allah (SAW), masu son kai da rashin tausayi. A wasu hadisan aka ce shugabannin za su kasance masu cakuɗa aikin kirki da na banza. Hadisan suna nuna gaskiyar annabtar Manzon Allah (SAW) domin kuwa ga abin da ya faɗi nan muna gani ƙeƙe-da-ƙeƙe.
In muka waiwayi ɓangaren umarnin da Manzon Allah (SAW) ya yi dangane da yadda za a mu'amalanci waɗannan irin shugabanni za mu ga cewa yake yi a yi haƙuri da su, a jure, a kai kuka wajen Allah, a yi musu ɗa'a matuƙar ba sun yi umarni da saɓon Allah ba. Sannan kuma Annabi (SAW) ya ce kar a yi fito-na-fito da su. Wasu hadisan kuma sun kwaɗaitar akan tunkarar su da nasiha ga wanda zai iya; wannan kam jihadi ne.
A wajen aiwatar da wannan umarni na Ma'aikin Allah (SAW), a nan gizo ke saƙa. Galibin mutane sun yarda cewa hadisan sun inganta, amma suna ganin ya kamata a duba fassarar, wasu na ganin cewa hadisan na magana ne akan shugaba wanda ke adalci, wasu na cewa sai in a gwamnatin Musulunci ne, wasu su ce ban da ƴan dimokuraɗiyya, wasu su ce zamanin aiki da hadisai irin waɗannan ya wuce, wasu su ce tun da yanzu shugabanni sun ɓoye ba a ganin su to a canza salo da dai sauran fassarori ire-iren waɗannan.
A iya ɗan ƙaramin sanina ban taɓa ji ko karanta maganar wani malamin hadisi da ya yi sharhin hadisan wanda da wata magana da za ta iya goyon bayan wani zance irin wannan ba. In na ce malamin hadisi ina nufin malamai irin su Baihaqiy da Tahawiy da Ibnul Jauziy da Nawawiy da Ibnus Salahi da Ibnu Taimiyah da Ibnu Muflih da Ibnu Rajab da Bajiy da Ibnu AbdilBarr da Qurtubiy da Iraqiy da Ibnul Mulaqqin da Badruddeen Al-'ainiy da Ibnul Hajrin da Shaukany da Ameerus-San'âniy kai da ma malaman zamanin nan namu irin su Mu'allimiy da Albaniy da Ibnu Bazz da Uthaimeen da Abdul Muhsin Al-Abbad da Ali Adam Al-Ityobiy da ire-irensu
Abin lura shine waɗannan fassarori na mu na gida; a bakinmu ake jin su, mu ne muka yi ma hadisan irin wannan fahimtar. Wataƙila yanayin da muke rayuwa a ciki na tsanani da rashin tausayi da ake gwada mana a tsarin da ake aiwatarwa shi ya taimaka mana wajen wannan fassarar.
Yana da kyau mu saba da sallama wa nassoshin Shari'a salamamwa muɗlaƙa ko da kuwa hakan ya saɓa wa abin da muke so, ko wanda muka saba ji, ko abin da wasu malamanmu suke akai
Wane gori ko raddi za ka yi wa wani 'ɗan bidi'a' ko ɗan tamore ko ɗan ƙala-ƙato ko waɗanda kake ce wa ƴan boko aƙida in ya zamana cewa kai ma akwai wasu hadisai da ka tsana? Akwai wasu nassoshin da ba ka son ka ji ana karantar da su?
Bin sunnar Manzon Allah (SAW) ba ya yiwuwa sai an sallama masa akan komai.
Allah Ubangiji ya sa mu dace.
0 Comments